SANA'AR WANZANCI.
Sana'ar wanzanci sana'a ce ta gargajiya wadda ake amfani da aska don aske gashi,da kuma yin kaciya da yin tsaga ko kaho saboda kawar da datti don samun lafiya ga al'umma.
Wanzami shi ne likitan da yake duba mutum in bai da lafiya ya ba shi magani a al'adance.
Ayyukan wanzami su ne;bada magani,yin aski,jarfa,kaho,kaciya,cire belu,cire suwa da gurya da sauransu.
Kayayyakin da wanzami ke aiki da su sun hada da:zabira,kaho,moda,aska,toka,
gwangwala,auduga da makamantansu.
Ta fuskar bayar da magani wanzami na amfani da ganyaye da sakesaki da suƴoƴi da wasu sassa na jikin dabbobi don samun lafiya ga marasa ita.
Magungungunan wanzami su;bagaruwa da gwanda suna maganin jini.Marin kusu na maganin cibi.Karya garma na maganin targade.Kitsen kaza na maganin karaya da sauran dangoginsu.
Wanzami na da amfani ga masarauta da kuma al'ummar gari.Hakan ta sa fada take nada sarkin aska da dangaladimarsa.Sannan wanzami na da amfani wajen bayar da magani da taskace al'adar gargajiya.Wanzami na da amfani ta fuskar karantarwa da tsoratarwa ga jama'a.
Tunanin Bahaushe dangane da wanzami shi ne,wanzami mutum ne wanda bai son abin da ya yi ai masa.Shi ya sa ake masa habaici da cewa wanzami bai son jarfa.Haka kuma Bahaushe ya dauki wanzami a matsayin likita.Shi ya sa yake masa kira ri kamar haka:
KIRARI:
Kalakala maganin gizo.
Wanzam aska na cikin kube tana cin gashi.
Kai wa sarki rotse ka tashi da girma.
Wanzam na sarkin aska wanda ba ka son a ga jikin ka.
No comments:
Post a Comment