Friday, 22 December 2017

SANA'AR WANZANCI.
Sana'ar wanzanci sana'a ce ta gargajiya wadda ake amfani da aska don aske gashi,da kuma yin kaciya da yin tsaga ko kaho saboda kawar da datti don samun lafiya ga al'umma.
Wanzami shi ne likitan da yake duba mutum in bai da lafiya ya ba shi magani a al'adance.
Ayyukan wanzami su ne;bada magani,yin aski,jarfa,kaho,kaciya,cire belu,cire suwa da gurya da sauransu.
Kayayyakin da wanzami ke aiki da su sun hada da:zabira,kaho,moda,aska,toka,
gwangwala,auduga da makamantansu.
Ta fuskar bayar da magani wanzami na amfani da ganyaye da sakesaki da suƴoƴi da wasu sassa na jikin dabbobi don samun lafiya ga marasa ita.
Magungungunan wanzami su;bagaruwa da gwanda suna maganin jini.Marin kusu na maganin cibi.Karya garma na maganin targade.Kitsen kaza na maganin karaya da sauran dangoginsu.
Wanzami na da amfani ga masarauta da kuma al'ummar gari.Hakan ta sa fada take nada sarkin aska da dangaladimarsa.Sannan wanzami na da amfani wajen bayar da magani da taskace al'adar gargajiya.Wanzami na da amfani ta fuskar karantarwa da tsoratarwa ga jama'a.
Tunanin Bahaushe dangane da wanzami shi ne,wanzami mutum ne wanda bai son abin da ya yi ai masa.Shi ya sa ake masa habaici da cewa wanzami bai son jarfa.Haka kuma Bahaushe ya dauki wanzami a matsayin likita.Shi ya sa yake masa kira ri kamar haka:
KIRARI:
Kalakala maganin gizo.
Wanzam aska na cikin kube tana cin gashi.
Kai wa sarki rotse ka tashi da girma.
Wanzam na sarkin aska wanda ba ka son a ga jikin ka.

Friday, 15 December 2017

HAWAN DABA(1).

Ma'anar Hawa.

Hawa ita ce sarrafa Doki a filin ta hanyar yin tafiya ko gudu.Haka kuma ana iya cewa Hawa buki ne da ake shiryawa don taya murna ga sarakai ko wasu manyan mutane ko kuma Angwaye da sauran su.

IRE-IREN HAWA.

-Hawan Salla

-Hawan Daushe

-Hawan Bariki

-Hawan Angunci

-Hawan Daba, dà sauransu.

 Tala'akari da haka wannan nazari zai mai da hankali ne a kan hawan Daba.

MA'ANAR HAWAN DABA.

W.A.E.C 2015,su ce, "Hawan Daba taron buki ne da ake shiryawa don sarakuna da manyan mutane don taya murna da kuma sada zumunta ga jama'a."

Ashe ke nan ana iya cewa hawan Daba bukin hawa ce da da ake yi ma wasu muhimman   don taya su murna.

MASU YIN HAWAN DABA.

Hukumar kula da jin dadin baki da shkatawa ita take shirya wa 

Sarakai,Hakimai,Gamnoni,'Yan ma'abba,Buwarai,kungiyoyin masu kide-kide da na al'adu da na tarihi da sauran su,sai kuma 'Yan kallo.

DALILAN YI.

Dalilin yi shi ne don taya sarki ko gwamna ko shugava kasa ko kuma wani gari murnar cikan shekaru a mulki ko kafuwa lafiya.Haka kuma ana yi don bunkasa al'adu da  sada zumunta ga al'umma.

WURIN YIN HAHAN DABA.

Yawanci an fi yin wannan taro a babban filin taro na tarayya ko na jiha wadda aka tanaza don gabatar da ire-iren wadannan taruka.Misali:A Abuja ana yi a filin taro na Egul.A Kano ana yin sa a fadar Sarki da kuma Fili taro na janaral Sani Abaca.A Kaduna ana yi a fadar sarkin Zazzau da kuma filin Janaral Murtala Ramat Muhammad da  sauran su.

LOKACIN YI.

Kowanne lokaci ana yin wannan hawa amma an fi yi da rana.Haka kuma wacannan hawa shekara shekara aka fi yi amma kafin shekara akan yi in har bukatar haka ta taso.

YADDA AKE HAWAN DABA.

Bayan an hada gangamin taro duk wadanda ake jjira sun zo, sai kowanne sarki da jama'arsa su fara wucewa suna zagaye filin.Daga nan kuma sai sarakuna su faara wucewa  ta gaban babban bako  ko bakuwa daya bayan daya suna kai gaisuwa,shi/ita kuma tana amsawa.Ita wannan hawa an tsara ta ce ta kasa mahaya rukuni-rukuni inda za su sukwano dawakai a guje don kai jafi ga manyan baki. Shi/su kuma wadanda aka kai masa/masu jafin suna kallon su.Bayan mahaya sun yi sai masu wasanni daban-daban su zo su nuna tasu irin fasahar.

KAYAYYAKIN YI.

Da fari akan shirya Dawakai da Rakumai ne na hawa da na Zage,wasu kuma sukan hada har da a motoci..Dawakan akan yi masu ado saboda kayatar da wurin bukin wadda in mai kallo ya gani zai yaba.Su kan su mahayan da mahalarta bukin ba a baya ba don kuwa sukan caba ado matuka. Sannan ga Masu,Kwalkwali,Garkuwai da sauran kayayyakin fada da na al'adu.Akwai kaysyyaki da dama da ake amfani da su.

WASU DAGA CIKIN GARURUWAN DA AKE YI.

Hawan Daba ana yi a Sakkwato,Zazzau,Kaduna,Kano,Katsina,Dsura,Bauci,Hadeja,Gobir,Bida,Abuja da wasu garuruwan Hausawa.

Misali a Kaduna a shekara 1949,zamanin sarkin Zazzau malam Ja'afaru dan Isiyaku an shirya wannan taro.Haka kuma a shekarar 1856,an shirya wa sarauniyar Ingil Elizabirth irin wannan hawa sakamakon ziyara da ta kawo wa jihar Arewacin Nijeriya.Manyan baki sun halarci wannan taro ciki har da sarkin musul.mai sir, Abubakar na II.

Makdi Salihu Jankidi ya bayyana mana hoton wannan hawa a cikin wakarsa dinda ya ce; 

"...Tun rad da Allah yat tsiri duniya ba a yi taro irin Kaduna ba.

-Da  Borno,Zazzau,har Adamawa.,Gwambe Katagum da Bsuci duk sun kawo jinjina.

-Birnin Kano da Hadejiya,ga KazaureKatsina sai murna suksi.

-Zamani nai sai shiy yin kira,kowa da kowa duk an hallara.

-Soja da 'Yandoka,Inyamurai,Jan Bature sun hi dubu dari bakwai.

-Har da 'Ya"yan na ta rawa cike, sahu biyar ne masu dawaki.

-Sarkin musulmi yad darzazo,wadansu na tafi wasu jinjina.

-Magaji mai farai ka hwada masu,uban sarakai duk Nijjejeriya..eh eh eh ehn!

-Zuwan Kaduna da an ka yi taro,sarauniya ta gode ma kwarai.

-Mutan Kaduna labari kowag ga Sakkwato ya gama kallo.

-Kayan Masar na birnin Hausa,wannan shiri haske sai alfijir.

-;Gimshimi dan Shehu Bakadire,na Bello sai Madi ko ba a so..."

Haka dai Sakihu Jankidi ya wake wacannsn hawa da manyan mutane da suka zo daga wasu garuruwa.Haka dai ake ta yin ire-iren hawan Daba Kaduna da wasu garuruwan.A shekarar ,2017 an yi wa sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris irinta don taya shi .murnar cika shekaru (42) lafiya a karagar mulki.Yau kuma ga shi a ranar Asabar ga watan Disamba,16/12/3017 za a sake gabatar da wata kan bukin cikar shekaru dari(100)da jihar Kaduna ta yi da kafuwa.

Majalisar masarautar Hadejiya ta taba shirya wa tsohon shugaban kasa Janaral Badamasi Baban Gida a kofar fadar sarki Alhaji Adamu Abubabakar Maje Haruna don karramawa.Haka kuma a Sakkwato a cikin watar Nuwamba shekara ta 2016 an yi wa sarkin .usulmai sa Sa'adu Abubakakar  na III hawan Daba.Guri ta jihar Bauci ma an yi hawa  Daba karo na farko ranar 8 ga watan Agusta,2013.A Kano a shekarar 1913, an yi wata gagarumar hawan Daba lokacin da sarki Eduward III ya kai wata ziyara garin Kanon.Haka a Gobir kungiyar(GDA) ta taba shirya taron hawa Daba a shekarar 2016, inda suka yi wa taron take kamar haka:

"Hawan Dabar halbin Bunsuru".Dabar sun shirya wa ne masana tarihi da suka je Gobir.

MANAZARTA:

-DailyTrust,(8/31/2012http:;//www.aminiyadailytrust.com.ng

-Hadejiya,(8/31/2012)Hadejiya Festibal.https://www.aminiyadailytrust.com.ng.

-Weekend, 14th, december:https://www.weekend,peoplesdailyng.com/index.

-W.A.E.C(june,2015)The West African Examination Council Pass Question paper Hausa paper II.http://www.waeconline.org.ng/elearning/Hausa/223q12html.

-NAFSES,(15/12/2017),Durbar In Kaduna.https://www..daikytrust.com.ng/infest-opens-with-durbar in kaduna ttml.